Hukumar yan sanda ta Nigeria wato Nigerian police force zasu fara physical screening da credential screening ranar ta daya ga watan February na shekarar 2022.
Related Nigerian police force sun fitar da final shortlisted na mutun dubu goma
Hukuma ta fitar da wannan sanarwanne saboda duk wanda yasan ya cika neman wannan aiki na dan sanda to yaje yayi physical screening kafun azo kan exams
Kuma wannan physical screening and credential screening da za ayi na dukka wanda suka nemi aikin ne bawai shortlisted akayi bah saboda haka idan kasan ka nema saika shirya wa zuwa screening da za ayi za afara ran daya ka watan February na shekarar 2022 a gama ranar ashirin ga watan February na shekarar 2022
Kuma wannan screening da za ayi kowa a garin da yacike a garin zaiyi bawai saika je wani gari ba don haka idan baka garin ka saika koma can domin a can zakayi.
Abubuwan da ake bukata wurin wannan screening dai kamai yadda akasa zakaje da farar riga da guntun wando da dai sauran su
Sannan zakasa takar dunka a cikin farin file takardun da ake bukata sune
1. National I'D card
2 O'level results
3. Certificate of birth/ declaration of age
4. Certificate of origin
5. Sai slip naka dakayi printing
6. Grantor's form
Idan bakada grantor's form koh kuma baka printing slip nakaba to kashiga https://policerecruitment.gov.ng/#/register kadakko
Sanna zaka zo da original sannan kuma kayi copy duda biyu
Duk wanda bai zo da wa yannan abubuwanbah kuma baza a saurareshi a matsayin wanda yaje screening bah.
Kuma wannan screening din kyautane ba a bada kudi kar wani ya yaudareka cewa ana biyan kudi.
Allah ya bada sa a
A.I.H
Idan kanada tambaya ka ajiye a wurin comment ko kuyi joinTelegram channel namu domin karin bayani koh tambaya.
1 Comments
Thanks.
ReplyDeleteAmma ka ce kowa a garin su, a gidan mai gari ko a police station ko kuma ina?