Hukumar zabe ta Nigeria wato Independent National Electoral commission wato INEC zata bara diban ma aikata na wucin gadi
Related: Yadda zakayi registration na TIN number
Yadda zaka hana wayanka kona yaranka ko wanni naka kallon batsa ta internet
Kamar dai yadda mutane suka sani duk bayan shekara huɗu idan lokacin zaɓe ya kusa to INEC tana diban sabbin ma aikata na wucin gadi da zasuyi aiki na wannan zaɓe da za ayi
To kamar dai na kowanne zaɓe wannan karonma INEC ta sanarda ranar fara diban wannan ma ai kata domin yin aikin zaɓe na 2023 da muke fuskanta
Za a buɗe portal dinne ran 14 ga watan Tara wato 14 September 2022 yau saura sati ɗaya kenan daidai sannan za a rufeshi ranar talatin ga watan sha ɗaya wato 30 November 2022.
Kuma rukunin aikin ya kasu kashi hudu ne kuma ko wanne da kalan matakin da ake buƙata kafun ka nemi wannan aiki wanda za suyi aiki na wucin gadi sune kamar haka:
1. SPOs- (Supervisory Presiding officers) shi wannan shine na farko wanda manya a aikin gwamnati ko na alumma suke cikewa wanda sai kakai GL10- GL14 koh kuma ma aikatan waƴannan hukumomi wadanda suka cancanta a NYSC, NOA da kuma NIMC. Harma da ma aikatan INEC din ita kanta
2. POs. APOs (I,II,III) (Presiding officers)na biyu shine POs da kuma matainakinsa na daya dana biyu dana uku matakin da ake buƙata domin cike wannan abun shine:- waɗanda suke service yanzu wato Cops members waɗanda suke bautar ƙasa kenan da kuma wanda sukayi sukayi bautar kasan suka gama a shekarun 2018, 2019, 2020, dakuma 2021 sai kuma ɗalibai da suke karatu a makarantin gaba da secondary kamar University, polytechnics da college of education da daisauransu na jaha kona ɠwamnatin tarayyan. Sannan MDAs ma aikatansu na dindindin wanda suke da OND ko kuma GL07- GL10.
3. RAC Managers (Registration Area)sukuma shugaban maƙarantin RAC koh ma aikatansu daga level GL07 zuwa sama
4. RATECHs (Registration Area Technicians) shi wannan ma aikatan INEC ta ɓangaren ICT sune zasuyi wannan aikin sai kuma ƴan bautan ƙasa da suke service a wannan ma aikatan ta INEC
Waɗannan sune matakai guda hudu da za a ɗibi wannan ma aikata akai saboda haka inkasan ka shirya saika zauna cikin shiri ana fara cikewa kaima ka cike kuma za a cike shine a online
Yadda zaka nemi aikin zaɓe na 2023
Za ka shiga wannan link din ne idan an buɗe ranar shahudu ga wata https://www.pres.inecnigeria.org koh kuma wanna https://inecnigeria.org
Idan an buɗe in Allah ya bamu iko zamu kawo muku yadda zaku cika da screenshot dalla dalla insha Allah.
Sannan wanda zai cika dole ya kasance baya da register da wata jamiyyar siyasa wato ba dan wata jamiyya bane
Sannan bazai numa koh bayyana wani danntakara a matsayin wanda yake goyon baya bah wato ba aso a samu corruption kenan
Sanna dole yakasance kana state din daka zaɓa a lokacin neman wannan aiki kar kana Kano ka cika Gombe
Allah ya bada sa a
✍️✍️✍️©️ A.I.H
Idan kanada tambaya ka ajiye a wurin comments section koh kuyi joinTelegram channel namu domin karin bayani koh tambaya.
0 Comments