Yadda zaka nemi aikin sojan ruwa wato Nigerian Navy

 Hukumar sojan ruwa ta Nigeria wato Nigerian Navy zasu fara ɗiban sabbin ma aikata 



Hukumar tana sanarda dukkan masu sha awan shiga wanna aiki cewa zata buɗe portal domin fara registration na Nigerian Navy Basic Training School batch 35 wanda zata buɗe ranar laraba 29 ga wannan watan sanna kuma za a rufe in sha Allah ranar asabar 6 ga watan biyar wato may 2023 in Allah ya kaimu 

Ga wasu daga cikin sharuɗan nema 

Dole yakasance kanada 5 credit a SSCE GCE NABTEB koh NECO kuma kada ya wuce zama biyu 

Sannan certificate na makaranta kada yayi sama da shekara shida 

Dole mai nema yakasance daga shekara 18 zuwa 22 ga masu SSCE saikuma masu NCE diploma Nurse/midwife, sportsmen and women dasu imam Driver mechanic sukuma daga shekara 18 zuwa 26 

Yadda zaka nemi aikin sojan ruwa wato Nigerian Navy

Da farko zaka shiga wannan link ɗin https://joinnigeriannavy.com saika cike dukkan abunda ake buƙata kai submit idan kuma baka iyaba kaje shagon computer mafi kusa dakai domin su cikema 

Wannan neman aikin kyautane bawani kuɗi da ake biya saboda haka akiyaye da macuta da zasuce ka kawo kuɗi koh wani abu makamancin wannan 

Allah ya bada sa a

Idan kanada tambaya ka ajiye a wurin comments section koh kuyi join Telegram channel namu domin karin bayani koh tambaya.

Post a Comment

0 Comments